ABNA24: Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, karfe 7 na safiyar yau Lahadi ne aka bude runfunan zaben 7277 a fadin kasar Syria domin zabar ‘yan majalisar dokokin kasar, inda tuni jama’a suka fara fitowa domin kada kuri’unsu.
‘Yan takara 1,656 ne suke fafatawa domin neman kujeru 250 na majalisar dokokin kasar ta Syria a wannan zabe, wanda zai ci gaba da gudana har zuwa karfe 7 na yammacin yau, duk kuwa da cewa akwai zaton cewa za a kara wa’adin matukar dai aka samu cunkoson jama’a domin bayar da dama ga kowa ya kada kuri’arsa.
Duk da cewa zaben yana gudana ne a wannan lokaci da ake fama da cutar corona, amma mahukuntan kasar ta Syria sun dauki kwararn matakai na kiwon lafiya a yayin gudanar da zabukan, kamar yadda kuma aka sanya ka’idoji wadanda dole ne mai kada kuri’a ya kiyaye su, kamar saka takunkumin fuska da kuma bayar da tazara.
342/